Jama'a barkanmu da war haka. A shirinmu na rana da misalin karfe biyu agogon Najeriya da Nijar, muna dauke da wadannan rahotannin:
- Najeriya: Hukumar zabe ta INEC ta kara wa'adin karbar kantin zaben da take rabawa.
- Nijar: An sanar da rufe wasu jerin kasuwanni a gundumar Abala da ke jihar Tillabery.
- Kamaru: Hukumomi sun ce kashi 46 cikin 100 na makarantu ne kadai ke aiki a halin yanzu a arewa maso yamma da kuma kudu maso yammacin kasar.
- Sharhunan Jaridun Jamus a kan nahiyar Afirka.
Shirye-shiryen Dandalin Matasa da kuma Ji Ka Karu za su biyo baya. Ku kasance tare da Tijjani Hassan.



Comments
Post a Comment